
Dan gwamnan jihar Borno mai suna Umara ya musanta zargin da wasu kafafen yada labaru ke yi masa kan kisan wani mutum a kasar Indiya.
Idan ba'a manta ba, gwamnatin jihar Borno tuni ta musanta zargin da ake wa dan gwamna Zulum kan kisan.
Kafafen sada zumunta kwanaki biyu da suka gabata, sun wallafa cewa Umara wanda dalibi ne a wata jami'a a birnin New Delhin kasar ta Indiya, ya kashe wani dan kasar Chana a gidan rawa kan wata budurwa.
Mai magana da yawun gwamna Zulum Abdurrahman Ahmed Bundi ya ce, babu wani daga 'ya'yan gwamna Zulum da aka kama ko ake zargi da laifin kisa a fadin duniyan nan.
Bundi ya ce, akwai bukatar al'umma su yi taka-tsan-tsan wajen saurara da yada labaru a shafukan sada zumunta.
A nashi bangaren, gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya yi tsokaci kan batun, inda ya ce zargin kawai aiki hannun makiya ne don su bata mishi suna.