• 17 Jun, 2025

Daga Yanzu Za A Iya Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima Kowace Ma'aikatar Gwamnati—Cewar Ministan Harkokin Matasa A Najeriya

Daga Yanzu Za A Iya Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima Kowace Ma'aikatar Gwamnati—Cewar Ministan Harkokin Matasa A Najeriya

1000011789.jpg


Gwamnatin Najeriya ta fara maida hankali kan matsalar rashin aikin yi ga matasan kasar, inda ta soke dokar da ta hana tura matasa masu yiwa kasa hidima wasu ma'aikatun gwamnati.

A wata wasika da ma'aikatar ci gaban matasa da ke dauke da sa hannun ministan kula da ci gaban matasa ya aikawa babban daraktan NYSC, gwamnatin tarayya ta sanarda soke dokar, ta yadda za a iya tura masu yi wa kasar hidima kowani ma'aikatan kasar.

Umarnin zai fara aiki ne daga rukunin 'C' na masu yiwa kasar hidima wanda ke tafe daga wannan wata na Nuwamba zuwa watan Disamban wannan shekarar ta 2024.

Ministan ma'aikatan kula da bunkasa matasan ya ce, daga yanzu kowani mai yiwa kasa hidima zai samu damar yin hakan a kowace ma'aikatan gwamnati a fadin kasar.

An dauki wannan matakin ne domin kawo karshen matsalar rashin aikin yi ga matasan wadanda su ne shugabanni nan gaba.

Daga yanzu, gwamnati ta soke  tsohuwar dokar da ya ce a tura masu yiwa kasa hidima bangarorin bada ilimi da noma da kiwon lafiya da ababen more rayuwa kadai.

Ministan ya ce, yanzu dai za a iya tura su kowani bangare a kasar wadanda su ka hada da bangaren man fetur da iskar Gas, da babban bankin kasar da sauran manyan ma'aikatu da a baya ba a tura masu yiwa kasa hidima guraren.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.