• 17 Jun, 2025

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tinubu Ta Sake Kara Kudin Litar Man Petur Yau Talata

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tinubu Ta Sake Kara Kudin Litar Man Petur Yau Talata

1000006365.jpg

Kamfanin mai na NNPCL a Najeriya ya kara kudin litar man fetur daga Naira 
1,030 zuwa Naira 1,060 a birnin tarayya Abuja.

Hakan ya faru ne yayinda wasu masu sayan man suka je wasu daga cikin gidajen man fetur na kamfanin a yau Talata.

Rahotanni sun nuna cewa ana sayarda man kan Naira 1,025 maimakon Naira 998 a birnin Legas da ke kudancin kasar.

Karin kudin litar man ya zo ne kasa da makwanni uku da kara kudin man.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.