
A kalla sojoji 7 sun hallaka sakamakon wata nakiya da ta tashi a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne bayan rundunar sojan Najeriya ta aika sojoji tarwatsa 'yan kungiyar Boko Haram da suka kai hari a wata kauye a jihar ta Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa motar sojan Najeriya ta taka wata nakiya da aka dasa kan tirin Gamboru-Ngala, inda ta amsa ta hallaka sojojin guda 7 a cikin motar su.
Rahotannin sun bayyana cewa soji guda daya ne cikin sojoji 8 dake cikin motar sojojin ya rayu bayan tashin nakiyar.
Motoci da dama dake kan titin yayin da nakiyar ta tashin sun lalace. An ruwaito sojojin Najeriya na ta fadi-tashi don tattara gawakin 'yan'uwansu da suka rigamu gidan gaskiya a iftila'in.
A cewar rundunar sojin Najeriya, motocin soja guda uku aka aikawa kauyen domin ceto al'ummar. Mota ta farko da ta biyu sun shige, amma ta karshe ce ta hau kan nakiyar.