
Kungiyar SERAP a Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kawo karshen dabi'ar Allah wadai da ministan Abuja Nyesom Wike da ma gwamnonin kasar 36 ke yi.
Kungiyar ta ce, ya kamata shugaba Tinubu ya dauki matakan gaggawa kan ministan da gwamnonin 36 dangane da ruguza bangaren Shari'a da su ke yi, ta hanyar bawa alkalan kotu toshiyar bakin motoci da gidaje domin hana su gudanarda ayyukan Shari'a a kasar yadda ya kamata.
Kungiyar ta ce lokaci ya yi da shugaban kasa zai dasa musu aya kan bada cin hancin motoci da gidaje na alfama da gwamnonin kasar da ministan Abuja ke yi.
A wata wasika da kungiyar ta rubutawa shugaban kasa Bola Tunubu a jiya Asabar, mataimakin Daractan kungiyar Kolawole Oluwadare, ya ce, hakan mummunan hali ne wanda kundin tsarin mulkin Najeriya bai amince da shi ba.
Kolawale ya ce, hakan zai hana bangaren Shari'a binciken 'yan siyasa yadda ya kamata da ma aiwatarda doka da oda akansu.
Kolawale ya kara da cewa gwamnonin da ministan babban birnin tarayya sun maida alkalan kotun kasar kamar yaran gidansu, inda darajar alkalan ya zube warwas.
Kungiyar ta SERAP ta ce lokaci ya yi da shugaba Bola Tinubu zai bawa ministan Shari'ar Najeriya Lateef Fagbemi umarni ya fara daukan matakan ladabtarwa kan gwamnonin da ministan Abuja Nyesom Wike.
Kungiyar ta ce, akwai bambanci wajen aiki tsakanin bangaren Shari'a da bangaren zantarwa da ma bangaren yin dokoki a kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kolawale ya ce, yin watsi da abinda gwamnonin da ministan ke yi babban hadari ne ga mulkin dimokuradiyya a kasar matukar shugaban kasa bai dauki matakan dakatarda hakan ba.
Kungiyar ta SERAP ta bayyana cewa ta kuma mikawa wakiliyar majalisar dinkin-duniya kan 'yancin alkalan duniya Ms. Margaret Sattetthwaite wasikar domin duba lamarin da zummar kawo canji.