
Yan Najeriya masu ajiyar kudade a wasu bankunan kasuwanci a kasar na kokawa kan yadda suka ce ana cire musu kudade daga asusun su ba tare da izini ba.
Sun kuma kara da cewa kawo yanzu babu wani kwakkwarar bayani daga mahukunta daga bangaren gwamnati ko bankunan daga kasa har sama.
Wasu daga cikin yan kasar sun bayyana cewar lamarin na dab da kassara harkokin kasuwancinsu da ma na yau da kullum.
Yan Najeriya dai na fama da matsalolin tattalin arziki tun hawar Shugaba Bola Tinubu karagar mulkin kasar, inda lamura suka rincabe.
Abin jira a gani dai shi ne ko gwamnatin kasar za ta kawo karshen lamarin duba da halin da yan kasar ke ciki na talauci ko akasin haka.