
Bankin Polaris tare da hadin gwiwar hukumar kula da tattala muhalli sun fara aikin dasa itatuwa a birnin Kano domin dawo da darajar birnin.
An fara aikin dasa itatuwan ne a Ajingi yankin kunkurawa a Kano ranar 30 ga watan Agusta da ya gabata.
Bankin Polaris dai ta fara wannan hubbasa ne a Jami'ar ilimi da ke Ijagun Ijebu Ode a jihar Ogun kudu maso gabacin Najeriya.
Shugaban bankin mai kula da yankin arewacin Najeriya Mahmud Kawu shi ya jagorancin aikin.
Mahmud Kawu wanda ya wakilci babban managan bankin Omokayode Lawal ya ce sun fara aikin ne domin ceto mutuncin muhalli, saboda itatuwa suna da daraja a ko ina a duniya.