
Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta yi Allah wadai da rawar da bankin lamuni na duniya wato IMF ke takawa wajen cusawa gwamnatin Najeriya tsare-tsare da su ka jefa yan kasar cikin masifar talauci da rashin tabbas.
Kungiyar ta kodago ta ce, IMF ce ta sa gwamnatin kasar cire tallafin man fetur da ya sa yan Najeriya suka zama mabarata a kasarsu.
Duk da cewar bankin lamunin na duniya ya musanta zargin, kungiyar kodago ta ce, tun ba yau ba IMF ya sa Najeriya cikin tarkonsa, don haka, zancen banza bankin lamunin ke yi.
Kungiyar kodagon ta ce bankin lamuni da bankin duniya sun dade suna neman tarwatsa tattalin arzikin kasar ta hanyar jefa Najeriya da sauran kasashe masu tasowa cikin wahalhalu.
Shugaban kungiyar kodagon Joel Ajaero ya gargadi bankin duniya da bankin lamuni da su fice daga idon Najeriya don kasar ta samu cigaba a matsayinta ta kasa mai yanci kamar kowa.
Ajaero ya ce, Najeriya ba ta bukatar bankin lamuni da bankin duniya a harkokinta. Ajaero ya kara da cewa, bankin duniya da bankin lamuni sun zama tamkar annoba ga kasashe masu tasowa a duniya.