• 17 Jun, 2025

Bankin Duniya Ta Ce Har Yanzu Najeriya Na Biyan Basukan Da Obasanjo Da Yar'adua Da Jonathan Suka Ciyo

Bankin Duniya Ta Ce Har Yanzu Najeriya Na Biyan Basukan Da Obasanjo Da Yar'adua Da Jonathan Suka Ciyo

depositphotos-384250048-stock-photo-world-bank-glass-building-mirrored.jpg

Bankin Duniya ta ce har yanzu Najeriya tana ci gaba da biyan basukan da shugabannin ta da suka gabata suka ciyo.

Bankin ta ce tana bin kasar zunzurutun kudi Dala biliyan 10.6 da tsofin shugabannin ta  Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Ya'adua da Goodluck Jonathan suka runtumo.

A cewar bankin, tsofin shugabannin Najeriyan sun karbi basukan har sau 69 yayin da shugabannin uku suke kan karagar mulkin kasar.

Hukumar kididdigar basuka ta Najeriya ta ce jimillar kudaden da kasar ta karbo bashi sun kai Naira triliyan 121.67 a nazarin basukan kasar da ta yi a watan Yunin wannan shekarar.

A nata bangaren, babban bankin kasar ta ce kawo yanzu Najeriya ta biya bashin Dala biliyan 15.55 daga shekarar 2019 zuwa yanzu.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.