
Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike ya ce, Shugaba Bola Tinubu ba dora shi kan kujerar minista don ya sayarda filayen mutane a Abuja ba, sai don ya kawo canji.
Nyesom Wike ya furta haka ne yayinda ya ke kaddamarda aikin gina titi na tsawon kilomita 15.5 a yankin Kwali da ke birnin Abuja jiya Talata.
Wike ya ce ya karbi kujerar minista ne don ganin an samu cigaba a birnin tarayya, inda ya ce burinsa a kullum bai wuce gyara Abuja ba.
Nyesom Wike ya ce Allah ya albarkaci al-ummar yankin Gomani da ke Kwali da kasar noma, don haka gina musu titin zai bunkasa harkar nomar.
Wike ya ce duk wanda yake kokwanto game da abubuwan da yake yi na kawo ci gaba a Abuja, ya bibiyi lamuran yadda ya kamata zai gane gaskiya.