
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce zai ci gaba da yin gwaji da makamai masu linzami samfurin Oreshnik mai gudu fiye da sauti.
Makamin mai linzami da aka harba ranar Alhamis an samu cikakkiyar nasarar yin gwajinsa a cewar Putin, inda ya bayyana cewa babu wata kasa a duniya da take da irin makaman da kasarsa ke da su.
Da yake magana yayin wata ganawa da jagororin tsaron kasar, Putin ya ce samar da sabbin makamai masu linzami dole ne bisa irin barazanar da suke fuskanta daga wasu kasashen duniya.
Shugaban Rasha ya kuma ce ba za a iya tare makaman masu linzami ba, inda ya ce, suna da irin wadannan makaman kuma a shirye suke su yi amfani da su a kowani lokaci idan bukatar hakan ta taso.
Vladimir Putin ya ce, ya bayar da umarnin kera sabbin makaman ba tare da bata wani lokaci ba, inda ya jaddada karfin kasar sa ta Rasha wajen tunkarar duk wanda ya takale su.