• 18 Jun, 2025

Babu Wata Hujja Da Ta Nuna Auwal Sankara Na Da Alaka Da Matar Aure—Cewar Wani Jami'in Hukumar Hisbah

Babu Wata Hujja Da Ta Nuna Auwal Sankara Na Da Alaka Da Matar Aure—Cewar Wani Jami'in Hukumar Hisbah

1000004245.webp

Wani jami'in hukumar Hisbah ta jihar Kano Malam Aliyu Dakata ya ce, babu wata hujja da ta nuna Auwal Danladi Sankara na da alaka da Tasleem Baba.

Hukumar Hisbah dai na zargin kwamishinan da gwamnan jihar Jigawa ya dakatar Auwal Danladi Sankara da laifin yin lalata da matar aure Tasleem Baba a birnin Kano.

Aliyu Dakata ya shaidawa manema labarai a jiya Talata cewa Auwal Danladi Sankara baida laifi domin babu kwakkwarar hujja akan hakan.

Aliyu Dakata ya ce, lokacin da jami'an Hisbah suka je wajen da ake zargin Auwal da Tasleem na lalata, sun tarar da Tasleem a cikin motar ta na yin waya, yayinda shi kuma Auwal Sankara ke tsaye a cikin wani gida da ake ginawa mallakar sa.

Aliyu Dakata ya ce, kawo yanzu babu wata hujja da ke da alaka da labarin farko na lalata tsakanin Auwal da Tasleem.

Aliyu Dakata ya kara da cewa zargin da ake yiwa Auwal Danladi Sankara ya sa ya rasa kujerar sa na kwamishina a jihar sa ta Jigawa.

Tun ranar Talata ne lauyan Tasleem Baba wato Rabiu Shuaibu ya ce, Tasleem ta samu sabani da mijinta sakamakon wat matsala na cikin gida.

Lauyan ya ce, Auwal Sankara ya rabu da Tasleem wata 10 da suka gabata, inda Tasleem ta fara harkar sayarda abinci.

Aliyu Dakata ya ce, ranar da ake zargin su da aikata badaidai ba, Tasleem ta je wajen Auwal Sankara ne domin ta kai mishi abinci da ya saya a matsayinta na mai sana'ar sayarda abinci.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.