
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Kaduna a matsayin wasan yara.
Jam'iyyar ta ce, Zaben da aka yi musamman a karamar Hukumar Kagarko a jihar ba zabe ba ne gaba daya.
Shugaban jam'iyyar na karamar Hukumar ta Kagarko Ahmadu Yusuf ne ya furta hakan yayinda ya ke taron manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Yusuf ya ce duk da cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ta sanarda jam'iyya mai mulki APC a matsayin wadda ka lashe zaben a Kagarko, babu wani zabe da aka gudanar, kawai ha'inci da rashawa aka tabka.
Ahmadu Yusuf ya kara da cewa a karamar Hukumar Kagarko dai babu wani zabe da aka yi sai dai kwace.