• 18 Jun, 2025

Babu Wani Dan Kabilar Ijaw Da Zai Zabi Tinubu, Za Mu Hada Kai Da Arewa A Zaben 2027—Cewar Asari Dokubo

Babu Wani Dan Kabilar Ijaw Da Zai Zabi Tinubu, Za Mu Hada Kai Da Arewa A Zaben 2027—Cewar Asari Dokubo

1000005521.jpg

Tsohon shugaban tsagerun Naija Delta Mujahid Asari Dokubo ya bayyana  shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin mayaudari mutum.

A wani faifayin bidiyo da Asari ya fitar, ya ce, ya bawa Shugaba Bola Tinubu gagarumin gudumawa wanda yakai shi ga cin zabe a shekara ta 2023, amma Tinubu ya watsa mishi kasa a idanu.

Dokubo Asari ya ce Shugaba Tinubu ya ajiye shi a gefe, inda ya manta da wahala da hadarin da ya jefa kansa akan Bola Ahmed Tinubu lokacin zabe.

Asari ya yi alwashin hada kai da yan siyasan arewacin Najeriya a zabe mai zuwa na 2027 domin rama abinda Tinubu ya yi mishi.

Asari Dokubo ya bayyana cewa ya na neman afuwan magabatan yankin Naija Delta kan laifin marawa shugaba Bola Tinubu baya da ya yi a zaben 2023.

Mujahid ya kara da cewa hadin kai da magabatan Naija Delta su ka yi da arewacin Najeriya a siyasance abu ne  mai kyau, don haka, shi ma daga yau zai bi sahun su.

Dokubo Asari ya ce, ya kwashe duk kudaden sa ya marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su, amma a yanzu haka, ko kallon sa Tinubu ba ya yi.

Mujahid Asari Dokubo ya ca, daga yau, babu wani dan kabilar Ijaw da zai  marawa Tinubu baya a zabe mai zuwa. Dukkansu za su yi aiki ne da yan arewa.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.