
Kwamitin wanzar da zaman lafiya karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja Abdussalam Abubakar ya ce har yanzu suna samun matsin lamba kan rashin nagartar zaben shugaba Bola Tinubu.
Kwamitin na tsohon shugaban sojan Najeriya Abdussalam Abubakar ya furta haka ne a jiya Juma'a a Abuja yayin da ya gabatar wa jama'a rahoto mai shafi 106 kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar na shekara 2023.
Kwamitin ya ce ana ta kai musu korafe-korafe da su tilasta wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta soke zaben da ya ayyana Bola Tinubu a matsayin mai nasara.
Kwamitin ya ce bukatun sun hada da soke zaben baki daya ko amince wa da kashi hamsin na sakamakon zaben kafin zaben ya zama mai nagarta.
Korafe-korafen zaben na da alaka da samun kashi 25% cikin dari daga jihohin kasar musamman a babban birnin tarayya Abuja inda aka samu rashin amincewa kan sakamakon zaben.
Kwamitin ya kara da cewa akwai kura-kurai matuka cikin yadda aka tattara sakamakon zaben da ya ayyana Shugaba mai ci Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe shi.
Kwamitin na zaman lafya ya ce akwai matsanancin korafe-korafe ta hanyar kiraye-kirayen ga kwamitin da ma hukumar zaben da su kai doki lokacin zaben sakamakon rashin nagartar sa.
Ai kai matakin da yan kasan sun bukaci Kwamitin da hukumar zaben kasa ta dakatar da tattara sakamakon zaben a lokacin da korafe-korafe ya yi yawa lokutan da ake tattara sakamakon zaben.