
Mai fafutukar kare hakkin bil-adama kuma jagoran neman canji Omoyele Sowore ya ce zanga-zanga ranar 1 ga watan Goma ta zama dole domin 'yanta Najeriya daga hannun azalumai.
Sowore ya ce ko da jami'an tsaro sun kama shi gudanar da zanga-zangar rashin mulki mai nagarta a kasar ya zama dole.
Mamallakin kafofin yada labaran Sahara Sowore ya furta hakan ne yayin zantawa da tashar talabijin na News Central TV a safiyar yau Litini.
Omoyele Sowore ya ce da zaran an fara zanga-zangar, ba za a dakata ba har sai gwamnati ta biya dukkan bukatun talakan Najeriya.
Sowore ya kara da cewa a shekarar 2019 ma Jami'an tsaro sun garkame shi amma hakan Bai hana yin zanga-zanga ba, a wannan karo ma babu mahalukin da zai iya hana zanga-zanga a Najeriya.