• 18 Jun, 2025

Babu Gwamnan PDP Da Bai Nemi Mukami A Gwamnatin Tinubu Ba - Cewar Nyesom Wike

Babu Gwamnan PDP Da Bai Nemi Mukami A Gwamnatin Tinubu Ba - Cewar Nyesom Wike

fb-img-17262953277333075.jpg

Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce gwamnonin PDP ba za su iya da shi ba saboda suma sun nemi mukamai a gwamnatin Bola Tinubu.

Wike ya bayyana haka ne yayin da ake hira da shi a tashar talabiji na Channels, inda ya ce shi ba barazana ne ga PDP ba.

A kwanakin nan ne dai Nyesom Wike ke ta rigima da gwamnonin PDP sakamakon kallon hadarin kaji da su ke wa juna.

Wike ya ce ya sanar da Jam'iyar PDP kafin ya karbi kojerar minista daga gwamnatin Bola Tinubu, inda Jam'iyar ta PDP ta amince mishi karban mukamin ministan daga gwamnatin APC.

Wike ya kara da cewa duk gwamnonin PDP sun nemi mukamai a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Nyesom Wike ya kalubalanci gwamnonin na PDP kan neman mukamai da suka yi a rubuce a gwamnatin Bola Tinubu.

Minista Wike ya ce, duk da cewa Jam'iyar APC ta ci zaben shugaban kasa a jihar Rivers amma PDP ce ta lashe zaben gwamna da kujerun majalisar dokokin kasa daga jihar.

Wike ya ce, shi dan PDP ne kuma ya yi bayani tun da farko cewa ba zai goyi bayan PDP a matakin zaben shugaban kasa ba domin ba su yi abinda ya dace ba.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.