• 17 Jun, 2025

Babu Farashin Man Fetur Kasa Da Na Matatar Dangote Da Ke Da Inganci—Cewar Mai Managa Da Yawun Matatar Dangote

Babu Farashin Man Fetur Kasa Da Na Matatar Dangote Da Ke Da Inganci—Cewar Mai Managa Da Yawun Matatar Dangote

1000008039.jpg

Matatar man Dangote ta ce babu wani man fetur da yan kasuwa za su shigo da shi kan farashi kasa da nata da ke da inganci.

Kamfanin na Dangote ya furta haka ne a martaninsa ga Kungiyar Masu Dakon Mai IPMAN dangane da korafinsu na tsadar man a kamfanin.

A makon da ya gabata ne dai Kungiyar ta IPMAN ta bayyana shirinta na fara shigoda tataccen man fetur daga kasashen ketare sakamakon tsadar sa a matatar Dangote.

Mai magana da yawun kamfanin na Dangote Anthony Chiejina ya ce, farashin man da kamfanin NNPCL ta sa babu wani tsada sabanin abinda kungiyar ta IPMAN ke cewa.

Anthony ya ce, duk wani man fetur da farashinsa ya gaza na Dangote, ba mai inganci ba ne a kasuwannin saya da sayarda mai a fadin duniya.

Anthony ya kara da cewa man fetur da yan kungiyar IPMAN ke shirin fara shigowa da shi na da hadari ga lafiyar dan'Adam domin ba a bin ka'ida wajen tace shi.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.