• 18 Jun, 2025

Babu Dan Bindiga Ko Jami'in Tsaro Da Ya Kama Ni - Cewar Malam Bello Yabo

Babu Dan Bindiga Ko Jami'in Tsaro Da Ya Kama Ni - Cewar Malam Bello Yabo

fb-img-17260361275546718-1.jpg

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan  Bello Yabo ya bayyana cewa 'yan bindiga ba su yi garkuwa da shi ba kamar yadda ake rade-radi.

Malam Yabo ya ce babu kuma wani jami'in hukumar tsaron farin kaya ta DSS da ya ziyarce shi da sunan kama shi.

Tun makon da ya gabata ne dai ake ta tura sakonni a shafukan sada zumunta inda wasu ke zargin 'yan bindiga sun kama malam Bello Yabo, yayin da wasu kuma ke cewa jami'an hukumar farin kaya ta DSS ne su ka kama shi.

Hakan ya sa masoyan Malam Yabo da dama a cikin Najeriya da ma wasu kasashen ketare  kira ta wayar salula domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Akarshe dai Sheikh Bello Yabo ya ce yana nan tare da iyalen sa cikin koshin lafiya. Malam Yabo ya kara da cewa jita-jita ne kwai mutane ke yadawa.

Malam Yabo ya ce wasu ne da ba sa furta alkairi ke danganta shi da 'yan bindiga da hukumar tsaro ta DSS.

Sheikh Bello Yabo ya shawarci mutane su rika tantance bayanai domin sanin ingancin su kafin su fara yada su.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.