
Babban sufeton 'yan'sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya haramta wa 'yan dokar Amotekun zuwa wajen zaben gwamnan jihar Ondo da ke tafe.
Zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa na jan hankulan 'yan siyasar Najeriya ciki da waje, inda jam'iyyoyi 17 ne za su yi takarar neman kujerar.
A wata sanarwa da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa Muyiwa Adejobi yau Lahadi, sufeton 'yan'sandan ya ce, tuni rundunar ta girke jami'anta na musamman domin tsaro ranar zaben.
Adejobi ya ce daga cikin rundunar ta musamman akwai 'yan'sandan kwantarda tarzuma da masu dakile ta'addanci da ma wata runduna ta musamman don tabbatarda cikakken tsaro ranar zaben gwamnan.
Muyiwa ya kara da cewa, akwai kuma tsaro da za a gudanar ta sama ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu domin karin tsaro.
Adejobi ya bayyana cewa hakan ya zama dole ne duba da muhimmancin samarda tsaro lokacin zaben jihar ta Ondo.
Muyiwa ya kara da cewa, rundunar 'yan'sandan za ta yi amfani da jiragen kwale-kwale domin tsaron yankunan da ke kewaye da koguna.
Muyiwa ya ce, babban sufeton Egbetokun ya yi alkawarin tabbatarda tsaro a kananan hukumomi 18 da ke jihar ta Onda gabani da bayan zaben gwamnan da za a gudanar ranar Asabar 16 ga watan Nuwamban nan.