• 18 Jun, 2025

Ba Za Mu Karbi Magudin Zaben Gwamna A Jihar Edo Ba - Cewar Jam'yyar PDP

Ba Za Mu Karbi Magudin Zaben Gwamna A Jihar Edo Ba - Cewar Jam'yyar PDP

fb-img-17263390222898924.jpg

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta gargadi jam'iyya mai mulki ta guji duk wani kokarin tada hargitsi a zaben gwamna da ke tafe a jihar Edo, kudu maso kudancin Najeriya.

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda ke jagorantar kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar PDP a jihar ta Edo,ya tabbatar wa 'yan jihar cewa zabe mai inganci ya zama wajibi.

Zaben gwamnan jihar ta Edo wanda za a gudanar a ranar 21 ga wannan watan na Satumba ya ja hankalin 'yan siyasar kasar, inda gwamna Fitiri  ya ce jam'iyyar PDP ba za ta lamunci magudin zabe ba.

Gwamna Fintiri ya ce jihar Edo jiha ce na wayayyun mutane masu ilimi, don haka ya zama dole a ba su abinda suka zaba.

A nashi bangaren, shugaban riko na jam'iyyar PDP Illiya Damagun ya yi alwashin jam'iyyar tasu za ta kare kuri'un su matukar sunci zabe, inda ya ce babu wani mahalukin da zai murde musu zabe.

Damagun ya gargadi hukumar zabe ta INEC ta guji hada baki da jam'iyya mai mulki ta APC wajen ayyana wanda baici zabe ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shawarci 'yan jihar Edo su jefa kuri'un su su kuma tsare batare da wani ya canja abinda aka zaba ba.

Yanzu haka dai jam'iyyar PDP na zargin gwamnatin APC da kama wasu 'ya'yan ta gabannin zaben gwamnan da ke tafe.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.