
Gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Rada ya ce ba zai tura jami'an tsaro domin kama wani idan ya zage shi ko ya ci mutuncin sa ba.
Gwamnan ya bayyana cewa akwai nauyin talakawa akan su, don haka babu dalilin da zai sa ransa ya baci don an zage shi kan abinda ya gaza yi a matsayin sa na shugaba.
Dikko Rada ya ce abu mai muhimmanci shi ne su duba korafe-korafen jama'a da zummar daukar wadanda za su iya gyarawa domin kawo canji.
Umaru Dikko Rada ya kara da cewa gwara talakawa su zage su a nan duniya domin su gyara maimakon jama'a su yi shiru su kyale su idan sun mutu su fiskanci tuhumar Ubangiji ranar kiyama.
Gwamna Rada ya umarci duka 'yan siyasar jihar Katsina da su kauda kunnuwa da idanun su daga damuwa da zagi ko cin mutunci domin shugabanci suke yi.
Gwamnan ya ce, idan basa shugabancin jihar Katsina babu wanda zai zage su ko ci musu mutunci. Amma tunda suna rike da shugabanci, dole ne su kauda idanu da kunnuwan su daga zage-zagen mutane.