• 17 Jun, 2025

Ba Za Mu Bari Seyi Tinubu Ya Zama Gwamna Ba, Jihar Legas Ba Ta Gado Ba Ce—Cewar Jam'iyyar Adawa Ta PDP Reshen Jihar Legas

Ba Za Mu Bari Seyi Tinubu Ya Zama Gwamna Ba, Jihar Legas Ba Ta Gado Ba Ce—Cewar Jam'iyyar Adawa Ta PDP Reshen Jihar Legas

1000012853.jpg

Jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Lagas ta ce, 'yan jihar ba za su zabi dan shugaban kasa Seyi Tinubu Gwamnan jihar Legas a zabe mai zuwa ba.

Hakan ya biyo bayan goyon baya da wasu kungiyoyi su ka yi na son ganin Seyi Tinubu ya gaji Sanwo-Olu a zaben shekara ta 2027 da ke tafe.

Daga daga cikin kungiyoyin a cewar jam'iyyar PDP, ta bada goyon bayanta kan Seyi Tinubu ya nemi kujerar gwamnan jihar ta Legas, wani taro da ta shirya ranar Talata a birnin Owerri a jihar Imo.

A cewar jam'iyyar PDP, wata kungiyar ma ta nuna goyon bayanta kan Seyi Tinubu ya nemi kujerar jagorancin jihar Legas, inda ta bayyana dan shugaban kasan a matsayin mutumin kirki, wanda zai kawo wa jihar ci gaba.

Duk da goyon baya da wasu ke nunawa kan batun, da dama daga 'yan jihar sun ce ba za ta sabu ba bindiga a ruwa, domin jihar ba ta Tinubu da iyalensa ba ne, inda su ka ce, ba za su bautawa uba sannan su bautawa dansa a jihar ba.

Mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP a jihar, Hakeem Amode ya ce, ba za su zabe shi ba, domin jihar Legas ba ta gidansu ba ce, inda ya ce, kujerar gwamnan jihar ba ta gado ba ce.

Hakeem ya ce, za su lalata duk wani yunkuri na maida dan Bola Tinubu gwamnan Lagas, domin Lagas ba kamar jihar Ondo ko Edo ba ne.

Hakeem ya kara da cewa, 'yan jihar Legas da dama ba su zabi Bola Tinubu,wanda hakan alama ce da ke nuna cewa Seyi Tinubu ba zai taba zama gwamnan jihar Legas ba.

Wata gamayyar matasa 'yan asalin jihar Legas sun bayyana cewa ba za su bar Seyi Tinubu ya zama gwamnan jihar ba fomin shi ba dan jihar Legas ba ne.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.