• 18 Jun, 2025

Ba Ni Da Naira Dubu Dari Lokacin Da Na Tsaya Takarar Gwamna—Cewar Wani Tsohon.Gwamna

Ba Ni Da Naira Dubu Dari Lokacin Da Na Tsaya Takarar Gwamna—Cewar Wani Tsohon.Gwamna

img-20240810-wa0066-554x536-1.jpg

Tsohon Gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ya tsaya takarar gwamna bai mallaki kudi Naira dubu 100 ba.

Shekarau ya furta haka ne yayin  ganawa da manema labarai kan bikin cika shekaru 70 na kungiyar dalibai Musulmai wato MSSN.

Malam Shekarau ya ce MSSN ta bada gudumawa mai yawa a ci gaban addinin Musulunci a kasar tsawon shekarun.

Ibrahim Shekarau ya ce babu wata tuhuma a kansa na cin hanci da rashawa. Don haka mutane su bar cece-kuce akan batun da babu kan gado.

Shekarau Ya kara da cewa, babu wanda ya taba bashi Naira daya tilo da sunan cin hanci tun daga ranar da ya hau kujerar gwamnan jihar Kano tsawon shekaru takwas.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.