
Duk lokacin da shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu a sabuwar dokar kere-kere a Najeriya, kasar za ta samu ikon fara kera albarusai da sauran makamai da rundunonin tsaro ke bukata a nahiyar Africa.
Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan harkokin tsaro ne suka bayyana haka yayinda suka kai ziyara Makarantar koyarda dabarun tsaro da ma kwalejin horasda hafsoshin sojan kasar da ke Kaduna.
Yayin zantawa da manema labarai bayan ziyarar tasu, shugaban kwamitin tsaron majalisar Babajimi Benson, ya ce, Najeriya na samun cigaba ta fannin kere-keren kayan yakin sojoji, wanda hakan zai rage dogaro da shigoda su daga kasashen ketare.
Benson, wanda shi ne ya jagoranci kudurin dokar a majalisa ya bayyana cewa idan Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu a dokar, kasar za ta samu tagomashi a duniya baki daya.
Shugaban kwamitin ya kara da cewa ya zama dole Najeriya ta tashi tsaye don ganin ta habbaka harkar kere-kere musamman kera kayayyakin yaki na sojojin, inda kasar za ta hada kafada da takororinta masu kere-kere a duniya.
Shugaban kwamitin ya kara da cewa akwai bukatar Najeriya ta zama kan gaba cikin kasashen nahiyar Afrika da ma duniya baki daya wajen kera kayan yaki domin ci gaban tattalin arzikin kasa.