
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce, abin takaici ne karbo bashin kudin da Shugaba Bola Tinubu zai yi, bayan basukan da kasar ke fama da su.
Atiku Abubakar ya furta haka ne bayan majalisar dattawan kasar ta amincewa shugaban kasa karbo bashin kudi har Naira triliyan 1.77.
Atiku ya bayyana cewa babu wani bashi da gwamnatin kasar karkashin shugabancin Bola Tinubu ta karbo ya amfani talakawan kasar.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kara da cewa bashin zai kara wahala ne akan wanda ke akan talakan kasar, musamman idan ba a yi amfani da kudin yadda ya kamata ba, wanda hakan ke da wuya.
Atiku ya ce, kasafin kudin shekarar 2024 baki daya na tattare da kura-kurai, inda ya ce, wannan bashin kudin ma wasu ne za su hadiye shi da sunan cike gurbin kasafin kudin bana.
A cewar Atikun, majalisar kasar sun zama tamkar 'yan amshin shata, inda ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta samu kudin shiga yadda ake bukata, amma duk da haka, za ta karbo bashi.
Atiku ya ce, babu bukatar karbo wani bashi a kasar da ke cikin matsin tattalin arziki da rashin shugabanci na gari.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kara da cewa, ya damu sosai duba da shekara daya da wani abu kadai shugaba Tinubu ya yi, amma ya tarawa kasar basuka, inda kasar ta zama ta uku a jerin kasashen da basuka su ka yi musu katutu a duniya.