
Ministan birnin tarayyar Najeriya Nyesom Wike ya ce Atiku Abubakar ba zai samu takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a zaben shekara 2027 ba.
Wike ya bayyana hake ne yayinda ya ke tattaunawa da 'yan jaridu a birnin Abuja jiya Talata, inda ya ce 'yan Najeriya ba sa bukatar tsohon mataimakin shugaban kasar a mulkin Najeriya.
Atiku Abubakar wanda ya yi takara da shugaba Bola Tinubu a zaben shekara ta 2023 ya ce, da shi ne ke mulkin Najeriya, 'yan kasar ba za su shiga halin ukuba da su ke ciki ba.
Wike ya ce, babu wata alama ko dama da Atiku Abubakar zai iya samu don hawa karagar mulkin Najeriya a zaben shekara ta 2027.
Nyesom Wike ya kara da cewa babu wata jam'iyya da Atiku zai samu tiketin tsayawa takarar zaben shugaban kasa mai zuwa.
Wike ya ce, a dai jam'iyyar adawa ta PDP Atiku ba zai taba samun dama ba, inda Nyesom Wike ya ce babu wata jam'iyya da za su bashi takarar shugabancin Najeriya.
Nyesom Wike ya kara da cewa Atiku Abubukar ya zama tsohon yayi, don haka, ya koma gida ya raka tsufarsa.