• 18 Jun, 2025

Ana Zargin Gwamnatocin Jihohin Kaduna Da Kano Da Katsina Da Karkata Tallafin Abinci Daga Gwamnatin Tarayya

Ana Zargin Gwamnatocin Jihohin Kaduna Da Kano Da Katsina Da Karkata Tallafin Abinci Daga Gwamnatin Tarayya

image-188.webp

'Yan jihar Kaduna da Kano da Katsina sun ce har yanzu ba su karbi shikafa da gwamnatin tarayya ta aikawa jihohin uku ba.

Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta aika buhunan shinkafa cike da  manyan motocin daukar kaya 20 ga kowace jiha a fadin kasar domin rage radadin yunwa da talakawa ke ciki.

Duk da kokarin gwamnatin tarayyar wajen rage wahalar abinci da 'yan Najeriya ke ciki, ana zargin wasu gwamnonin kasar da karkata kayayyakin abincin zuwa bukatun su.

Wasu daga birnin Kaduna sun nuna rashin jin dadin su inda suka ce ba su ga ko kwano guda na shinkafa da sunan tallafi a jihar Kaduna ba. Sun ce sunji labari ne kadai amma ba su gani ba.

Wani mai suna Salisu Musa da ke zaune a unguwar Rigasa da ke birnin Kaduna ya ce yanada iyali amma babu wanda ya bashi ko kwano guda na shinkafa a jihar. Ya ce baida labarin bada tallafin shinkafa.

Salisu Musa ya ce, duk da cewa yana kusa da masarautar gargajiya a jihar ta Kaduna amma bai ga wata shinkafa da sunan tallafi ba.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.