• 17 Jun, 2025

Ana Asarar Naira Triliyan 1 A Najeriya Sakamakon Shigo Da Littafai Daga Kasashen Ketare—Cewar Adekinle

Ana Asarar Naira Triliyan 1 A Najeriya Sakamakon Shigo Da Littafai Daga Kasashen Ketare—Cewar Adekinle

1000007272.jpg

Kungiyar Masu buga littafai a Najeriya sun bukaci agajin gaggawa daga mahukunta sakamakon tabarbarewar harkar.

Kungiyar ta ce tana asarar a kalla kudin shiga da ta kai Naira triliyan guda a kowace shekara a kasar sakamakon rashin kudaden aiki.

Shugaban kungiyar Adekinle Adebambo ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da kungiyar ta shirya a babban birnin tarayya Abuja.

Adebambo ya ce, mafi yawancin kamfanonin nasu sun durkushe sakamakon rashin kudi da yanayi.

Shugaban kungiyar ya ce akwai bukatar agajin gaggawa daga gwamnatin Najeriya don ceto harkar daga rugujewa baki daya.

Adebambo ya ce, idan gwamnati tayi hubbasa wajen bada agajin da ake bukata, za a samu canji.

Shugaban ya kara da cewa Najeriya na asarar kudi Naira biliyan 200 kowace shekara don shigoda littafai da  kayayyakin buga su daga kasashen ketare.

Adebambo ya ce, duk lokacin da mutum ya je filayen tashi da saukar jiragen saman Najeriya, zai tararda manyan jirage da ke shigoda littafai da kayayyaki da ke da alaka da buga su.

Adekinle Adebamno ya ce, akwai dunbun daliban sakandare a kasar da kowanne ke sayan littafai 9 a takaice domin nazari, wadanda ya kamata ana bugasu ne a Najeriya, amma hakan ya ci tura.

Adekinle ya ja hankalin gwamnatin Najeriya dangane da duba lamarin da idanun basira don kawo karshen matsalar, duba da muhimmanci harkar a kowace kasa mai son cigaba a fadin duniya.

 
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.