• 18 Jun, 2025

An Tsaurara Makatan Tsaro A Birnin Kano Sakamakon Rahotannin Da Suka Nuna 'Yan Ta'adda Na Boye A Sassan Birnin

An Tsaurara Makatan Tsaro A Birnin Kano Sakamakon Rahotannin Da Suka Nuna 'Yan Ta'adda Na Boye A Sassan Birnin

1000001262.jpg

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro a birnin Kano bayan da wani rahoton da hukumomin tattara bayanan sirri suka gano cewa akwai barazanar tsaro a birnin na Kano.

An tabbatar da haka ne sakamakon yanzu haka dimbin yan bindiga da suka tsere daga Zamfara ne ke fakewa a cikin birnin wanda shi ne mafi girma a arewacin kasar.

Ƴan ta'addar da suka tsere daga Zamfara na yi wa Kano barazana ta fannin tsaro duba da yadda harkokin tsaro suka tabarbare.

Rahotanni sun nuna cewar run ranar Litinin da ta gabata ne aka gabatar wa gwamnan jihar Kano da wannan rahoto, da ke cewa mafi yawan yan bindigar tuni suka mallaki gidaje a cikin birnin Kano.

Akwai bayanai da suka nuna cewar wasu na fakewa a unguwannin Rijiyar Zaki, Tudun Yola, Ja'en, Dorayi Babba, Rijiyar Lemo da kuma Yan Awaki. 

Daga dukan alamu dai rahoton ya ce mafi yawan yan bindigar na dauke da muggan makamai masu hadari.

Abin jira a gani dai shi ne ko gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya za su dauki matakan gagawa domin dakile barazanar ta tsaro.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.