
Hukumar samarda wutar lantarki a Najeriya ta bayyana cewa an samu raguwar karfin wutar kasar a cikin sakiyar wannan shekara ta 2024.
Hukumar ta ce karfin wutar lantarkin a farkon shekarar ya fi yadda yake a tsakiyar shekarar.
Hukumar ta kara da cewa wutar ta ragu daga abinda ya ke kasa 8,887.93Gwh zuwa 8,776.55Gwh a madatsar wutar ta kasa daga baya.
Abin nufi wutar ta ragu daga 4294.10MW zuwa 2294.29MW a cikin shekarar 2024.
A cewar hukumar wutar, abinda ake samu a kowani awa guda shima ya ragu daga 4069.57MWh/h zuwa 387.56MWh/h.
Hukumar ta ce abinda ake samu a kowani awa guda a madatsar wuta da ke Zungeru ya ragu matuka da kashi -9.52%5.
Hakan ya faru ne a cewar hukumar sakamakon raguwar karfin wutar daga madatsun wutar lantarkin na kasa.
Rahoton hukumar wutar ya bayyana cewa madatsar wutar Olorunsogo da Dadin Owo da Geregu da ma Shiroro su ne suka gaza bada wutar yadda ake bukata.
Haryanzu dai Najeriya na ci gaba da fiskantar kalubale a fannin samarda wutar lantarki mai dorewa sakamakon rashin maida hankali wajen sa kudi da yin abinda ya kamata.