• 18 Jun, 2025

An Sace Shugaban Hukumar NYSC A Najeriya

An Sace Shugaban Hukumar NYSC A Najeriya

screenshot-20240808-094232-1723106706497-1723106781110.jpg

Hukumar yiwa kasa hidima ta NYSC ta ce an sace shugaban ta na jihar Akwa Ibom Christopher Okun a kan hanyar sa ta ayyukan yau da kullum.

Anyi garkuwa da Okun ne tare da matukin motar sa mai suna Effiong Asibong yayin wata tafiya da ta shafi aikin ofishin shugaban.

Mai magana da yawun Hukumar ta NYSC Eddy Megwa ne ya bayyana haka a Abuja lokacin da yake zantawa da manema labarai akan lamarin.

Megwa ya ce anyi garkuwa da su ne yayin da suke kan hanyar su ta zuwa jihar Delta dake kudu maso kudancin Najeriya.

Eddy Megwa ya ce kawo yanzu dai babu wani labari mai ma'ana game da inda jami'in nasu da matukin sa suke duk da kokarin da Hukumar NYSC ta yi.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.