
A safiyar yau ne masu zanga-zanga suka fito kan titunan birnin Kano, yayin da suka hadu a Gidan Murtala daura da tashar motocin Kano Line.
Matasan dake dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban sun bayyana abubuwa da dama da suke bukata gwamnatin tarayyya ta gyara a kasar.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun shida wa manema labarai cewa za suyi tattaki daga Gidan Murtala zuwa titin Jiha domin zuwa gidan gwamnatin jihar Kano.
Matasa sunce za su mika wa gwamnatin tarayya bukatun su ta hannun gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf.
Kasuwanni da ofisoshi a birnin na Kano sun kasance a rufe a safiyar yau Alhamis sakamakon shirin zanga-zangar ta yau Alhamis 1 ga watan Agusta.