
An rufe Jami'ar tarayya ta Maiduguri wato UNIMAID sakamakon ambaliyar ruwa da ta hadiye wasu sassan birnin.
Ambaliyar ta haddasa asarar rayuka da dukiya kama daga gidaje zuwa guraren kasuwanci da kadarorin gwamnati a birnin.
Hukumar Jami'ar ta Maiduguri ce ta sanar da matakin rufe Jami'ar wanda mai kula da daukar dalibai Ahmad A. Lawan ya sa hannu.
Hukumar Jami'ar ta ce ta rufe Jami'ar na wani lokaci ne domin bawa al-ummar Jami'ar da ma ta jihar baki daya damar samun nitsuwa.
Hukumar Jami'ar ta jajanta wa malamai da daliban ta wadanda iftila'in ambaliyar ruwan ya shafa da ma al-ummar jihar ta Borno.
Jami'ar za ta ci gaba da kasance wa a rufe na wani lokaci domin kawar da fargabar da ke tattare da mutane.
Fashewar Dam din Alau ne musabbabin ambaliyar ruwan bayan ya cika fiye da kima da ruwa. Sakamakon haka ne ruwan daga dam ya nufi cikin birnin babu kakkautawa inda ya haddasa asara da dama.
A baya dai Dam din Alau ya taba fashewa ashekarar 1994 kimanin shekaru 30 kenan yau.