• 18 Jun, 2025

An Mika Sunan Kudirat Domin Jagorantan Kotun Kolin Najeriya

An Mika Sunan Kudirat Domin Jagorantan Kotun Kolin Najeriya

screenshot-20240815-161237-1723734787371-1723734805349.jpg

Hukumar kula da aikin alkalanci a Najeriya NJC ta bada sunan Mai Shari'a Kudirat Motonmori Kekere-Ekun a matsayin wadda za ta zama alkaliyar alkalan kotun kolin kasar.

Mai magana da yawun NJC Soji Oye ne ya bayyana wa manema labarai hakan a cikin wata takardar sanarwa da ya sanyawa hannu a yau Alhamis a Abuja.

Mai Shari'a Kekere-Ekun ta fara aikin alkalanci ne da kotun Magistrate ta jihar Lagas inda har ta kai matsayin babbar alkaliyar kotun kolin jihar ta Lagas.

Ta taba jagorantan kotu ta musamman kan fashi da makami da amfani da makamai ba bisa ka'ida ba a shekara ta 1996 har zuwa shekarar 1999.

Ta zama alkaliyar kotun daukaka kara a shekara ta 2004. A karshe ta zama daya daga cikin alkalan kotun kolin kasar a shekarar 2013.

An yanke shawarar mika sunan Kekere-Ekun ne bayan ganawa ta 106 da hukumar kula da harkar Shari'ar ke yi wadda babban alkalin alkalan Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya jogoranta.

Anyi ganawar ne ranar 14 jiya da 15 yau kafin ritayar babban alkalin alkalan kotun kolin Ariwoola wanda ake sa ran zaiyi ritaya ranar 22 ga wannan watan Agustan.

Tsohon shugaban kasa Muhamnadu Buhari ne ya nada Olukayode Ariwoola a matsayin alkalin alkalai ranar 21 ga watan Satumban shekarar 2022 domin jagorantan kotun kolin Najeriya.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.