• 18 Jun, 2025

An Kama Yar Shekaru 30 Da Makamai Cikin Buhun Hatsi

An Kama Yar Shekaru 30 Da Makamai Cikin Buhun Hatsi

fb-img-17238793128488817-1.jpg

Rundunar tsaro ta musamman ta kama wata mai shekaru 30 buye da makamai  a  yankin jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya.

An cafke Hauwa Yusuf ne yayin da ta boye bindigar AK-47 and gidan albarusai guda hudu a buhun abinci.

Hauwa Yusuf ta amsa laifin ta'addanci inda ta ce daya daga cikin manyan jagororin yan bindiga Aminu Basullube ne ya aike ta karbo makaman.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce anyi nasarar kama Hauwa Yusuf ne yayin binciken yau-da-kullum da yan sanda ke gudanar wa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Hauwa Yusuf dai yar garin Dutsin-Ma ce a jihar Katsina kuma an kama ta ne a kan hanyarta ta zuwa jihar Katsina daga Lafiya babban birnin jihar Nasarawa a cikin wata mota kirar Seinna.

Yayin da yan sanda ke mata tambayoyi, Hauwa Yusuf tayi ikrarin ba ta san abinda ke cikin buhun ba. Ta ce sako kawai aka ce ta karbo.

Ta ce an bata 130,000 kudin kai sakon da kuma 15, 000 na mota. Ta kara da cewa  ita gari ta gani a cikin buhun ba makamai ba. Hauwa Yusuf ta ce ta girgiza yayin da ta ga makamai a tsakiyar buhun garin.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.