
'Yansandan kasar Canada sun cafke wata 'yar Najeriya da ke zama a kasar mai suna Amaka Patience Sunnberger sakamakon barazanar da ta yi na hallaka wasu mutane daga kasar ta Najeriya.
Amaka ta yi barazanar hallaka 'yan kabilar Yoruba da Benin a wani bidiyo da ta aika shafukan sada zumunta.
Rundunar 'yansandan Toronto ne suka bayyana wa manema labarai hakan ta shafin su na yanar gizo.
'Yansandan sun sha alwashin gurfanar da Amaka Patience a gaban kuliya don hukunta ta daidai da laifin da ta aikata bisa dokar kasar ta Canada.
A ranar 25 ga watan Agusta ne Amaka ta aika wani sakon bidiyo inda ta ci akwashin hallaka al'ummomin kabilun na Yoruba da Benin.
Yanzu haka dai Amaka mai shakaru 46 na nan hannun 'yansandan Toronto tana jiran fiskantar hukunci.