
Gwamnatin jihar Kano ta kafa dokar hana fita a fadin jihar sakamakon tashin hankali da zanga-zangar lumana ya zama.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya furta hakan yayin taron manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kano a jiya Alhamis.
Gwamnan yace dokar hana fitan ta zama wajibi duba da yadda zanga-zangar da aka shirya na lumana ta rikide zuwa sace-sacen dukiyar gwamnati da na al'umma.
Abba Kabir Yusuf yace, matasa sun buge da kone-kone da sace-sacen kayayyakin da ba mallakin su ba wanda hakan ya tilasta aka samu asarar rayuka a zanga-zangar.
Gwamnan ya umarci jami'an tsaro a jihar ta Kano su tabbata dokar hana fita ta yi tasiri a fadin jihar domin dawoda zaman lafiya da doka da oda.
A jihar Yobe, Gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita a karuruwan Gashuwa da Potiskum da Nguru na tsawon awanni 24 sakamakon sace-sace da wasu matasa suka aikata.
Mai bawa Gwamna shawara kan harkokin tsaro Dahiru Abdussalam ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai.
Wani lamari dake da alaka da tashin hankali a jihar Borno shima ya tilasta gwamnatin jihar ta Borno kafa dokar hana fita a karamar hukumar Konduga, bayan yan kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyen Kauri suka hallaka mutum 16.