• 18 Jun, 2025

An Hango Mazauna Garin Akamkpa Da Ke Jihar Cross River Na Warwason Man Fetur Bayan Tankar Mai Ta Fadi

An Hango Mazauna Garin Akamkpa Da Ke Jihar Cross River Na Warwason Man Fetur Bayan Tankar Mai Ta Fadi

1000004520.jpg

An hango wasu daga cikin mazauna karamar hukumar Akamkpa da ke jihar Cross River, kudu maso kudancin Najeriya na dibar man fetur bayan wata tankar mai ta fadi a gefen hanya.

Rahotanni sun bayyana hakan ne a yau Alhamis bayan wasu sun dauki hotunan bidiyon abinda ya faru.

Hukumar kare hadura a Najeriya FRSC ta gargadi cews, ya kamata hukumomi su rika sa ido akan kowace tankar mai gabani da bayan daukar mai kafin hawa hanya domin rage matsalar faduwa da gobarar tankokin mai a kasar.

Kawo yanzu dai babu rahoton rasa rayuka a garin na Akamkpa da ke jihar ra Cross River.

A ranar 15 ga wannan watan ne dai irin wannan ta faru inda aka samu iftila'in rasa rayuka bayan faduwar tankar mai a garin Majia a karamar Hukumar Taura, da ke jihar Jigawa, inda mutum sama da 180 suka rasa rayukansu wasu kuma da damu suka jikkata, yayin diban mai bayan tankar ta fadi.

A karshe tankar ta yi bindiga inda wuta ta kona mutane 90 kurmus. Wasu karin mutanen kuma suka riga mu gidan gaskiya bayan an garzaya da su asibiti, inda adadin mamatan yakai 180.

Akwai bukatar gwamnati ta dauki matakai masu tsauri kan dauko man fetur cikin tankokin mai da ma duba lafiyan tankokin da hanyoyin da tankokin man ke bi domin kawo ceton rayukan yan Najeriya.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.