• 18 Jun, 2025

An Fito Zanga-Zanga Rana Ta Biyu A Abuja

An Fito Zanga-Zanga Rana Ta Biyu A Abuja

fb-img-17225972674152374.jpg

Masu zanga-zanga a Najeriya sun fito titunan babban birnin kasar Abuja a kokarin su na neman saukin rayuwa ga mahukuntan kasar.

Yau Juma'a rana ce ta biyu ta zanga-zangar da aka fara jiya Alhamis a fadin kasar sakamakon halin kunci da talakan kasar ke ciki.

Masu zanga-zangar dai sunce sun kosa da mulkin danniya da ake gudanar wa a Najeriya tun dawowar kasar tafarkin dimukradiyya a shekarar 199.

Yan kasar sun bayyana yadda abubuwa suka tabarbare a Najeriya duk da dumbun arzikin da Allah ya yi wa kasar dake yankin Afrika ta yamma.

Jami'an tsaro dai sun yi kokarin dakatar da mutane yin zanga-zangar musamman jiya Alhamis amma hakan bai yiwu ba.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.