
Wani mazaunin garin Bauchi, mai suna Muhammad Ibrahim ya soke aurensa da ya shirya yi da Fatima Abdulqadir.
Muhammad Ibrahim ya sanarda soke auren nasa ne a shafinsa ta sada zumunta ta Facebook ranar 21ga wannan watan na Nuwamba.
Auren dai an shirya yinsa ne a ranar 29 ga wannan watan, inda ya lalace kwanaki takwas kafin ranar daura shi.
Soke auren dai na da nasaba da gwaji da su ka yi wanda ya tabbatarda mijin na layin masu cuta sikila wato AS, yayinda matar ma ke layi guda na AS bayan ta yi gwaji.
Ibrahim ya karanci fannin kula da dabbobi a jami'ar jihar Bauchi, inda ya tabbatarda ya na da cutar sikila a watan da ya gabata bayan gwaji a asibitoci daban-daban.
Yanzu dai auren Ibrahim da Fatima ya ci tura, bayan sun shafe shekaru uku suna soyayya, inda su ka yi kuskuren gwaji tun farko.