
Matasa sun fara gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja a yau Lirini.
Matasan dai sun datse hanyar Abuja zuwa Kaduna a yunkurin su na neman canji a kasa.
Matasan dake dauke da kwalaye sun ambaci yunwa da tsadar abubuwa a kasauwa da rashin imanin talakawa daga jami'an gwamnati.
Masu zanga-zangar sun kuma ambaci tsare-tsaren da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo da ke maida talaka kamar bawa a kasar shi da sauran matsalolin da talaka ke ciki.