• 18 Jun, 2025

An Dakatarda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano

An Dakatarda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano

1000002141.jpg

Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta sanarda dakatarda Sakataren jihar Abdullahi Baffa Bichi daga kojerar sa.

Jam'iyyar ta kuma sanarda dakatarda kwamishinan kula da sufurin jihar ta Kano Muhammad Diggol daga mukamin sa.

Shugaban jam'iyyar NNPP ta Jihar Kano Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya tabbatarda hakan a jiya litini da yammaci.

Tuni faifayin bidiyon da shugaban jam'iyyar ta NNPP ya sanarda dakatar da sakatare da kwamishinan jihar ya karada shafukan yanar gizo da na sada zumunta.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewar dakatar da mutanen biyu daga mukamansu ya biyo bayan rashin ladabi ga jam'iyya.

Shugaban jam'iyyar ya kara da cewa mutanen biyu na amfani da mukaman su ta hanyoyin da basu kamata ba, da ma neman haddasa rigingimu a cikin jam'iyyar mai mulki a jihar ta Kano.


Hashim Sulaiman ya ce, matakin da jam'iyyar ta dauka na dakatar da mutanen biyu shi ne abinda ya kamata su yi a wannan lokaci domin su samu damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi musu.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.