
Jami'an tsaro sun ceto dalibai 20 da aka yi garkuwa da su, yayinda suka hallaka daya daga cikin masu garkuwa da daliban da ke koyon aikin jinya a Najeriya.
Jami'an tsaron hadin gwiwa da suka hada da 'yansanda da sojoji da jami'an tsaron sirri DSS sun yi nasarar ceto daliban Jami'o'in Maiduguri da Jos da aka yi garkuwa da su makonnin da suka gabata.
Daliban dai na kan hanyar su ta zuwa Enugu ne domin halartan wani taron kungiyar daliban ilimin aikin jinya karkashin lemar darikar Katolika ta addinin Krista inda suka hadu da iftila'in.
Sufeton 'yansandan Najeriya Kayode Egbetokun ne ya dauki matakin ceto daliban bayan 'yan Najeriya sun nuna hushin su kan lamarin.
Jami'an tsaron dai sunyi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu da ma wasu kayan aiki a kasa tare da ma'aikatan su domin gano inda aka ajiye daliban da aka yi garkuwa da su.
A karshe aka gano suna wani daji ne da ke yankin karamar hukumar Ado a jihar Benue, inda aka jikkata daya daga cikin masu garkuwan yayin da aka cafke mutum 2.
Tuni dai an garzaya da daliban jami'ar Maiduguri da Jos da aka ceto cibiyar jinya ta hukumar tattara bayanan sirri wato NIA domin duba lafiyar su.