
Ambaliyar ruwan sama ta hadiye dakunan koyo da koyarwa na jami'ar tarayya dake Birnin Lafiya.
Ambaliyar ta lashe tsangayoyi da dama na jami'ar a Jihar Nasarawa, arewa maso tsakiyar Najeriya.
Wani dalibi dan aji biyu wanda ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana cewa, ambaliyar ta illata karatun su.
Dalibin ya ce, har yanzu dalibai da dama basa iya zuwa azuzuwa koyon karatu saboda ambaliyar ta lalata abubuwa masu muhimmanci da ake bukata don koyo da koyarwa.
Dalibin ya kara da cewa, jarabawa na nan tafe amma dalibai ba su san matsayin su ba, sakamakon iftila'in ambaliyar.
Dalibin ya tabbatar da cewa, wasu malamai a waje suke gudanar da ayyukan koyarwa. Wasu malaman ma basa shiga azuzuwa koyarwa.