• 18 Jun, 2025

Al'ummar Jihar Delta Sunyi Korafi Kan Malalar Danyen Mai A Muhallan Su

Al'ummar Jihar Delta Sunyi Korafi Kan Malalar Danyen Mai A Muhallan Su

gettyimages-1126236314-612x612.jpg

Al'ummomin kauyukan karamar hukumar Warri ta kudu maso yamma a jihar Delta sun nuna damuwar su kan malalar danyen mai a matsugunin su.

Hakan kamar yadda suka bayyana na janyo musu illoli da suka shafi ruwan sha da koguna da ma albarkatun ruwa kamar irin kifi da sauran su.

Al'ummomin na yankin Naija Delta sun ce fashewar bututun mai na wasu kamfanoni masu aikin hako danyen mai ne sanadin matsalolin da suka tsinci kansu a ciki.

Al'ummomin sun ce kamfanonin na nuna halin rashin imani wanda hakan ya tilasta musu yin korafi akan lamarin.

Gamayyar al'ummomin yankin wanda wani mai suna Eric Omare yake  jagoranta ta mika korafin ta ga kamfanonin masu hako mai da ma kamfanin mai na kasa NNPCL da kuma gwamnatin jihar Delta domin neman doki.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.