• 18 Jun, 2025

Allah Ya Yi Wa Wani Basarake Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Wani Basarake Rasuwa

oba-aromolaran-1.jpg

Basaraken masarautar Ijesa da ke jihar Osun  Owa Obokun Oba Gabriel Adekunle Aromolaran ya rasu.

Oba Gabriel mai shekaru 86 ya rasu ne sakamakon gajerar rashin lafiya. Oba Gabriel Adekunle ya shafe shekaru 42 a kan karagar mulkin masarautar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo sun mika sakon ta'aziyyar su kan rashin.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya girgiza matuka game da mutuwar basaraken.

Mai magana da yawun shugaban kasan Bayo Onanuga ya bayyana cewa Bola Tinubu ya yaba da halaye masu nagarta tattare da mamacin yayin da yake raye.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa basaraken mutum ne na kowa domin kowa nashi ne, inda ya ce al-ummar masarautar za su shafe lokaci mai tsawo su na tunawa da marigayi Oba Gabriel Adekunle.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.