• 18 Jun, 2025

Al-Ummar Wani Kauyen Sunyi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Ta Gina Sabon Gada

Al-Ummar Wani Kauyen Sunyi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Ta Gina Sabon Gada

fb-img-17258564863730254-1.jpg

Mazauna kauyen Namnai da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba sunyi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta sake gina gadar Namnai da ta karye.

Gadar ta karye ne a watan Agusta da ya gabata sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi akai akai a cikin watan.

A skekarun baya dai sashi guda na gadar ya tsage, inda gwamnatin jihar lokacin mulkin Darius Dickson ta yi gyara domin lallaba gadar.

A karshe gadar Namnai ta karye baki daya ta yadda mutane da motoci ba za su iya hawa gadar ba.

Dan majalisar wakilan kasar mai wakiltan mazabar Bali da Gassol Ja'afaru Yakubu Chiroma ya samar da babban jirgin kwale-kwale na inji da ke tallafawa jama'a domin tsallake kogin.

Gadar Namnai ita kadai ce gada da ta hada kudu naso gabacin Najeriya da arewa maso gabas.

Abin jira a gani dai shi ne martanin gwamnatin tarayya kan gyaran gadar ko  akasin haka duba da muhimmancin gadar ta fiskar tattalin arzikin kasa.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.