
Shahararren dan kasuwan nan kana mamallakin matatar mai a Najeriya Aliko Dangote ya ce majalisar zantarwa ta kasa da kamfanin mai na NNPCL ne ke da alhakin ayyana farashin litar mai.
Rahotanni sun ruwaito cewar matatar mai na Dangote ce za ta yanke hukumcin yadda farashin litar mai zai kasance daga wata mai kamawa.
Rahotannin sun bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta mallaka wa matatar man Dangote ikon sanya farashin litar mai a kasar daga wata mai zuwa.
Mai bawa shugaba Tinubu shawara kan harkar yada labaru a nasa bangaren ya ce, ko da gwamnati ta bawa matatar man Dangote ikon sanya farashin litar mai, dole ne matatar ta sanya farashi domin samun riba.
Ya ce, matatar man Dangote ba za ta sayar da man petur kasa da farashin kasuwa ba kamar yadda mutane ke tunani.
Ya kara da cewa Dangote ya shiga harkar mai ne fa domin samun riba ba asara ba.
Daga yanzu dai 'yan kasuwa za su iya sayan mai kai tsaye daga matatar man Dangote batare da wani shinge ba.