• 17 Jun, 2025

Akwai Bukatar Najeriya Ta Ari Salon Zaban Shugabanni Irin Ta Kasar Sin—Cewar Gwamna Zulum

Akwai Bukatar Najeriya Ta Ari Salon Zaban Shugabanni Irin Ta Kasar Sin—Cewar Gwamna Zulum

1000008357.jpg

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bada shawarar amfani da salon kasar Chana wajen zaban shugabannin a Najeriya.

Babagana Zulum ya ce akwai bukatar Najeriya ta ari dabaru da kasar Sin ke amfani da su wajen fidda shugabamni a kowani mataki a kasar domin samun shugabanni masu inganci.

Zulum ya ce matukar anyi amfani da salon na kasar Chana, Najeriya za ta samu habaka ta fuskar shugabanci na gari.

Zulum ya ce, tsarin zaben kasar Chana na bada damar zakulo mutanen kirki domin su zama shugabannin, sabanin yadda ake bawa mutane mulki a Najeriya.

Gwwmna Zulum ya ce, kasar Sin na samun shugabanni ne ta hanyar bibiyar tarihin mutum da mukaman da ya rike a baya, da kwararan shaidu da suka nuna shi mutumin kirki ne kuma mai rikon amanar da aka bashi, kafin kasar ta Sin ta zakulo shi ta sanya shi cikin yan takara.

Zulum ya yi kira ga yan Najeriya da su fara rajin shugabanci na gari kamar yadda kasar Chana ke yi, inda ya ce, ya kamata yan kasar su zama mabiya masu gaskiya da rikon amana a kowani lokaci.

Gwamna Zulum ya ce, shugabannin Najeriya na da nasu matsalolin rashin iya shugabanci, amma talakawan kasar ma na taimakawa wajen lalacewar shugabanci a kasar.

Gwamna Zulum ya kara da cewa babu wani cigaba da Najeriya za ta samu mai ma'ana matukar babu shugabanci mai nagarta a dukkan matakai.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce akwai bukatar a rungumi fasahar aikin noma domin kaiwa ga gaci, inda ya ce, fasahar noma na da muhimmanci wajen bunkasa abincin da ake nomawa a Najeriya.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.